Benzema na shirin sauya ƙungiya a Saudiyya

[ad_1]



Rahotanni daga Saudiyya sun nuna cewa fitaccen ɗan wasan gaba na ƙasar Faransa, Karim Benzema, na tattaunawa domin komawa Al-Hilal bayan samun saɓani tsakaninsa da ƙungiyarsa ta yanzu, Al-Ittihad.

Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓangarorin, inda Al-Hilal ke son ɗaukar Benzema na tsawon watanni shida da suka rage masa a kwantiraginsa da Al-Ittihad.

Sai dai wakilin ɗan wasan na neman kwantiragin shekara guda da rabi.

Benzema, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2022, ya zura ƙwallaye takwas a wasanni 14 da ya buga wa Al-Ittihad a gasar lig ta Saudi Pro League a bana, amma bai buga wasanni biyu na baya-bayan nan ba.

Gaba ɗaya ƙungiyoyin biyu — Al-Hilal da Al-Ittihad — na ƙarƙashin mallakin Asusun Zuba Jari na Gwamnatin Saudiyya (PIF).

Rahotanni na nuni da cewa Benzema ya nuna rashin jin daɗi kan tayin tsawaita kwantiragi da kulob ɗin ya yi masa.

An ruwaito cewa daraktan wasanni na gasar Saudiyya, Michael Emenalo, ya miƙa wa Benzema wani tayin da ɗan wasan ya ɗauka a matsayin “wulaƙanci”, inda ya bayyana cewa tayin ya yi kama da buga wasa kyauta, sai dai haƙƙin hotunansa kaɗai, kamar yadda na kusa da shi suka bayyana.

Tsohon ɗan wasan ƙungiyar Lyon mai shekaru 38 ya koma Saudiyya a 2023 bayan shafe shekaru 14 yana taka leda a Real Madrid.

A kakar da ta gabata, ya ci ƙwallaye 21, lamarin da ya taimaka wa Al-Ittihad lashe kofin Saudi Pro League.

A bana kuma, Al-Ittihad na mataki na shida, inda take biye da Al-Hilal da ke jan ragamar teburin gasar da tazarar maki 12 a tsakaninsu.

Kocin Al-Ittihad, Sergio Conceição, ya ƙi yin tsokaci kan rashin haskawar Benzema a wasannin baya-bayan nan, inda ya ce: “Sai dai a tambayi shugabancin ƙungiyar.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *