Daƙile Taron Ƙasa Na Abuja: Ɓangaren PDP Ƙarƙashin Turaki Ya Caccaki Ɓangaren Wike
[ad_1]
Jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ta caccaki Kwamitin Riƙon Ƙwarya na Ƙasa da ke samun goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, bisa zargin da suka yi na cewa suna shirin hana gudanar da taron ƙasa a Abuja ta hanyar amfani da umarnin kotu a Ibadan.
Bangaren PDP mai samun goyon bayan Wike ya zargi ɓangaren Turaki da yunƙurin samun umarnin kotu daga Ibadan, Jihar Oyo, domin dakatar da taron ƙasa da za a yi a Abuja.
- Kano Pillars Ta Doke Enyimba, Ta Matsa Gaba A Teburin Gasar NPFL
- Tinubu Ya Yi Alƙawarin Ƙara Ƙaimi Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, (bangaren wike) na kwamitin riƙon ƙwarya, Jungudo Haruna Mohammed, ne ya bayyana zargin yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Wannan zargi ya zo ne kwana ɗaya kacal bayan bangaren Wike ya ƙaddamar da kwamitin shirya taron ƙasa, gabanin taron da za a yi ranar 29 ga Maris a Abuja.
In ba a manta ba, bangaren Wike a baya-bayan nan ya samu hukuncin kotu da ya soke taron ƙasa na Ibadan da aka gudanar a watan Nuwamba na bara, wanda ya samar da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Turaki.
Sai dai, da yake mayar da martani kan zargin da bangaren Wike ya yi, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na bangaren Turaki, Kwamared Ini Ememobong, ya yi watsi da zargin.
[ad_2]
Source link