Eid-el-Fitr:Kwankwaso Ya Buƙaci Magoya Bayansa Su Ci Gaba Da Jajircewa Kan Kyawawan Manufa
[ad_1]
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Kwankwaso, ya bukaci magoya bayan Kwankwasiyya da sauran magoya bayansa a siyasa da su ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da kyawawan manufarsu da suka hadu a kanta.
Kwankwaso ya yi wannan kira ne a ranar Litinin yayin da ya karbi bakuncin dubban magoya bayansa da abokan siyasa a gidansa da ke Kano, a lokacin ziyarar gaisuwar Sallah ta shekara-shekara.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X da aka tabbatar a ranar Litinin, tsohon gwamnan Jihar Kano ya jaddada bukatar ci gaba da nuna aminci da kuma taka rawar gani a harkokin siyasa.
Kwankwaso ya kuma yaba da halartar manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, da kuma ‘yan majalisun tarayya da na jiha da suka halarci taron.
[ad_2]
Source link