Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

[ad_1]


Babban Hafsan Sojan Kasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, a ranar Talata, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya samun ingantaccen tsaro a duk fadin kasar bayan tattaunawarsa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Da yake magana da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa bayan taron sirri, Babban Hafsan Sojan Kasa ya ce, bitar da ya yi kan ayyukan tsaro da ake gudanarwa, musamman bayan ziyarar da ya kai Arewa maso Gabas kwanan nan, ta nuna Zaburantarwa a ci gaba da yaki da ta’addanci.

Da aka tambaye shi, shin me ‘yan Nijeriya za su yi tsammani a cikin makonni masu zuwa, sai ya amsa da cewa, “Ingantaccen tsaro a fadin kasar.”

Laftanar Janar Shaibu ya bayyana cewa, bayanin da ya yi wa Shugaban Kasa, ya yi ne kan sakamakon rangadin aikinsa na yankin Arewa maso Gabas da kuma sabbin bayanai kan yanayin tsaro a fadin kasar.

“Na zo ne domin in yi masa bayani kan sakamakon ziyarar da na kai yankin Arewa maso Gabas sannan da kuma bitar wasu yanayin tsaro a fadin kasar, wanda hakan ya gamsar a wannan lokacin,” in ji Babban Hafsan Sojan Kasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *