Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
[ad_1]
Bisa labarin da aka bayar, majalisar harkokin kare hakkin dan Adam ta MDD ta shirya yin bincike kan yanayin kare hakkin dan Adam na kasar Amurka a zagaye na hudu, amma wakilan kasar Amurka sun ki halartar zaman, inda hakan ya janyo aka kasa gudanarwa.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Talata 11 ga wata cewa, batun ya shaida cewa kasar Amurka ba ta sa lura ga kare hakkin dan Adam, kuma ta nuna baki biyu wajen amfani da tsarin MDD.
Lin Jian ya yi nuni da cewa, tsarin binciken yanayin kare hakkin dan Adam muhimmin tsari ne da babban taron MDD ya ba da iznin kafa shi don kara yin mu’amala da hadin gwiwa wajen kare hakkin dan Adam, ya kamata dukkan kasashe membobin MDD su halarci binciken da ba da rahoto kan yanayin kare hakkin dan Adam nasu, da kuma sauraron ra’ayoyi daga bangarori daban daban. Kasar Sin ta kalubalanci kasar Amurka da ta koma halartar zaman binciken, da amincewa da aikin sa-ido daga bangarori daban daban, da kuma magance matsalolin keta hakkin dan Adam da suka shafe ta.
Ban da wannan kuma, game da batun cewa kasashen kungiyar EU suna shirin cire na’urorin kamfanonin sadarwa na kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin suna aiwatar da ayyukansu bisa doka a nahiyar Turai na dogon lokaci, wadanda suka samar da kayayyaki da hidimomi masu inganci ga jama’ar Turai, tare da samar da muhimmiyar gudummawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da samar da ayyukan yi a nahiyar. Kasar Sin ta kalubalanci kungiyar EU da ta samar da yanayin gudanar da ciniki cikin adalci da rashin nuna bambanci ga kamfanonin kasar Sin don magance wargaza amannar da kamfanonin suka yi wa nahiyar Turai kan zuba jari. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link