Farashin mai ya sauka bayan Trump ya miƙa wa Iran tayin sulhu
[ad_1]
Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya ragu da sama da kashi 5 a ranar Laraba, bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya miƙa wa Iran tayi da tsare-tsaren sulhun da za su yi domin kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya.
A cewar bayanai daga kasuwannin duniya, farashin man nau’in Brent ya sauka da kusan kashi 5.92 zuwa dala $98.30 kan kowacce ganga, yayin da nau’in West Texas Intermediate (WTI) ya ragu da kashi 5.01 zuwa dala $87.72.
Saukar farashin na zuwa ne bayan Trump ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa ana dab da kawo ƙarshen yaƙin da ya shafe kusan wata guda, tare da cewa Iran na shirin barin jiragen man fetur na ƙasashen da ba sa gaba da ita su riƙa wucewa ta Mashigar Hormuz.
A kasuwannin Asiya kuma, an samu hauhawar darajar hannayen jari, inda manyan kasuwannin Nikkei 225 na Japan da Kospi na Koriya ta Kudu suka tashi da sama da kashi 3.
Duk da alamun sassauci a diflomasiyya, har yanzu ana fuskantar tashin hankali a yankin, inda wani makami mai linzami daga Iran ya jikkata mutane a Isra’ila, yayin da ita kuma Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a wurare daban-daban ciki har da kudancin Lebanon.
Masana kasuwa sun ce raguwar farashin mai na nuna cewa ‘yan kasuwa sun fara rage fargaba, sakamakon yiwuwar samun sulhu da zai kawo ƙarshen rikicin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link