‘Yan Majalisar Kano 2 Sun Rasu A Rana Ɗaya
Jihar Kano ta shiga cikin jimami bayan rasuwar mambobinta guda biyu a ranar Laraba.
An ruwaito a baya cewa Hon. Aminu Sa’adu, wanda ke wakiltar ƙaramar hukumar Ungogo ne ya fara rasuwa bayan fama da rashin lafiya.
- Gwamnatin Tarayya Ta Ci Amanar ‘Yan Nijeriya Bayan Sauya Dokokin Haraji – Atiku
- A Karo Na 7 Sin Ta Gano Mahakar Mai Da Ke Dauke Da Mai Ton Miliyan 100 A Tekun Bohai
An garzaya da shi asibiti amma ya rasu a can.
Labarin rasuwarsa ya jefa ‘yan siyasa da jama’a cikin jimami a jihar.
Bayan sa’o’i kaɗan, Hon. Sarki Aliyu Daneji, wanda ke wakiltar ƙaramar hukumar Birni, shi ma ya rasu.
Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamnan Kano, ya tabbatar da rasuwarsa a shafinsa na Facebook.
Ya rubuta, “Innalillahi Wa Inna Ilaihirrajiun. Hon. Sarki Aliyu Daneji, memba mai wakiltar ƙaramar hukumar Birni a Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya rasu a yau sa’o’i kaɗan bayan rasuwar abokin aikinsa.”
Rasuwarsu ta girgiza abokan aikinsu, al’umma, da masu lura da harkokin siyasa.
Har yanzu Gwamnatin Jihar Kano ba ta fitar da cikakken bayani kan yadda mambobin suka rasu ba.