CMG Ya Gudanar Da Bikin Gabatar Da Nagartattun Shirye-Shiryensa A Kasashen Ketare

[ad_1]

Tsarin abota na watsa shirye-shiryen Sinanci da babban rukunin gidajen talabijin da rediyon kasar Sin wato CMG ya kafa a watan Afrilun bana, ya gabatar da jerin bukukuwan nuna shirye-shirye da mu’ammalar al’adu, da huldar dandalin al’adu, matakan da suka taka muhimmiyar rawa wajen watsa kyawawan al’adun gargajiya na Sin, da ba da labarai game da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje da na zamanantar da kasar, da kuma inganta karfin watsa shirye-shirye na mabambantan harsuna a duniya.

Kwanan nan, CMG ya kammala bikin gabatar da nagartattun shirye-shirye a kasashen ketare na shekarar 2025 bisa hadin gwiwarsa da abokan dake cikin wannan tsari. Kungiyoyi fiye da 60 ciki har da manyan kafofin yada labarai na kasa da kasa, da cibiyoyin koyon Sinanci a kasashen waje, da cibiyoyin yada al’adun Sin a kasashen waje daga nahiyoyi biyar na duniya, sun gabatar da nagartattun shirye-shirye sama da 30 a dandaloli 90 tun daga watan Satumba, wanda ya samu masu kallo fiye da miliyan 600 daga kasashe 90 da yankunan Hong Kong, Macau da Taiwan na Sin.(Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *