’Yan Bindiga Sun Kai Hari Tare Da Kashe Ɗan Kasuwa A Kano
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari garin Tiga da le ƙaramar hukumar Bebeji a daren ranar Litinin a Jihar Kano.
Sun kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Habibu Mai Shago, a cikin shagonsa.
- Da Gaske Ne Wasu Jami’ai 16 Sun Yi Yunƙurin Kifar Da Gwamnatin Tinubu — DHQ
- Dalilan Da Suka Sa Na Sauya Sheƙa Zuwa Jami’yyar APC – Gwamnan Kano
Har ila yau, sun sace kayayyaki sannan suka tsere.
Harin ya jefa mazauna garin cikin tsoro, inda suka nuna damuwa game da ƙaruwar hare-haren a ƙauyukan.
Wani masanin harkokin tsaro, mai suna DanKatsina50 ne, ya wallafa labarin a shafinsa na X.
Al’ummar yankin sun bayyana Alhaji Habibu Mai Shago a matsayin mutumin kirki, mai aiki tuƙuru kuma mai son zaman lafiya.
Har yanzu, hukumomi a Jihar Kano ba su fitar da wata sanarwa game da harin ba.
Mazauna garin sun roƙi hukumomin tsaro da su tura ƙarin jami’ai domin kare su daga hare-haren ‘yan bindiga.
A baya-bayan nan dai, yankunan da ke maƙwabtaka da jihar Katsina na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, lamarin da ya sanya gwamnatin Kano da ta Tarayya tura jami’an tsaro, domin kare al’umma.
[ad_2]
Source link