Dalilan Da Suka Sa Na Sauya Sheƙa Zuwa Jami’yyar APC – Gwamnan Kano
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC a hukumance bayan ficewa daga jam’iyyar NNPP da aka zaɓe shi a cikinta a 2023.
An sanar da komawar tasa ne a wani taro da aka yi a gidan gwamnati, inda manyan shugabannin APC suka halarta, ciki har da Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Barau Jibrin da Sanata Kawu Sumaila.
- Sheikh Joaan Ya Zama Sabon Shugaban Kwamitin Olympics Na Yankin Asiya
- An Yi Bikin Murnar Kaddamar Da Shekarar Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Ta Sin Da Afirka Ta Mauritius
Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin Jihar Kano ta samu damar cin gajiyar manyan ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.
Ya ƙara da cewa ya yi hakan ne bayan tuntuɓar abokansa na siyasa da wasu daga cikin kwamishinoninsa da ‘yan majalisa.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya bar NNPP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su haɗa kai wajen ciyar da jihar gaba ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
[ad_2]
Source link