Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa

[ad_1]



Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.

Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.

Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.

Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.

Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.

Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.

Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *