Trump Ya Ce Amurka Za Ta Ci Gaba Da Yaƙi Da Iran Ba Tare da Taimakon Kowa Ba
[ad_1]
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa ba ta buƙatar taimakon wasu ƙasashe wajen yaƙin da ta ke yi da Iran, musamman kan buɗe mashigar ruwan Hormuz.
A wani saƙo da ya wallafa, Trump ya bayyana cewa sojojin Amurka sun samu nasara, don haka ba sa buƙatar taimakon ƙasashen NATO, Japan, Australia da Koriya ta Kudu.
- CAF Ta Soke Nasarar Senegal, Ta Ayyaṇa Morocco A Matsayin Zakarar AFCON Ta 2025
- Tinubu Ya Bai Wa Masu Riƙe Da Muƙamai Da Ke Son Yin Takara Wa’adin Yin Murabus
Ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu ƙawayen Amurka suka ƙi taimaka mata, duk da cewa Amurka na da dubban sojoji a ƙasashensu domin kare su.
Wasu ƙasashe kamar Faransa, Jamus, Spain da Birtaniya sun ce ba za su shiga yaƙin ba, saboda ba yaƙin NATO ba ne.
Wannan mataki ya fusata Trump, inda ya ce Amurka za ta ci gaba da yaƙin ita kaɗai, yana mai cewa tuni suka fara samun nasara.
[ad_2]
Source link