Gwamna Abba Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar ’Yan Majalisar Kano 2

[ad_1]

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar alhininsa game da rasuwar mambobi biyu na Majalisar Dokokin Jihar da suka rasu a rana guda.

’Yan majalisar sun haɗa da Hon. Sarki Aliyu Daneji, wakili karamar hukumar Birni, da kuma Hon. Aminu Sa’adu, wakilin ƙaramar hukumar Ungoggo.

Gwamnan ya bayyana rasuwar tasu a matsayin babban rashi mai raɗaɗi ga Jihar Kano.

Ya ce ’yan majalisar shugabanni ne masu jajircewa da suka yi wa al’ummarsu hidima da gaskiya da ƙwazo.

A cewarsa, rashinsu zai bar giɓi mai girma a Majalisar da kuma cikin al’ummominsu.

Gwamna Abba ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansu, mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano, da kuma al’ummar ƙananan hukumomin Birni da Ungoggo.

Ya roƙi Allah Ya gafarta musu kurakuransu, Ya sanya su a Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansu da al’ummar Kano haƙurin wannan babban rashi.

Tuni aka yi jana’izar Hon. Aminu Sa’adu a maƙabartar Ungoggo, yayin da ake sa ran gudanar da jana’izar Hon. Sarki Aliyu Daneji a ranar Alhamis.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *