Amurka Za Ta Ƙaƙabawa Wasu ‘Yan Nijeriya Takunkumi

[ad_1]


Amurka ta ce za ta fara ƙaƙabawa wasu ’yan Nijeriya takunkumin hana su biza saboda zargin hannu a hare-haren da ake kai wa Kiristoci.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar ranar Laraba, an ce takunkumin zai shafi duk wanda ake zargin ya kai hari, ya ba da umarni, ya tallafa, ko ya tsoma baki cikin cin zarafin ’yancin yin addini.

Matakin na iya shafar iyalan waɗanda abin ya shafa.

Sanarwar ta ce matakin ya yi daidai da sashe na 212 na dokar shige-da-fice ta Amurka, kuma zai iya zama ruwan dare a Nijeriya da sauran ƙasashen da ake keta ’yancin yin addini.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Amurka da Nijeriya ke tattaunawa kan hare-haren ’yan ta’adda da ke ta kashe mutane.

A baya, Amurka ta zargi gwamnatin Nijeriya da mara baya ga masu kai wa Kiristoci hari, lamarin da ya jawo barazanar Shugaba Trump na kai wa Nijeriya hari.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *