Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia
[ad_1]
Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu, ba ta shafi batun sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC ba, sai dai a kan shugaban ’yan awaren ƙungiyar Biyafara, Nnamdi Kanu.
Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ferdinand Ekeoma, ya fayyace cewa ziyarar ta biyo bayan iƙirarin tsohon Kwamishinan jihar Charles Ogbonnaya.
Tsohon Kwamishinan, ya ce Gwamna Otti ya gana da Tinubu ne don tattaunawa shirin sauya sheƙarsa zuwa APC kafin zaɓen 2027.
“Gwamnan ya gana da Shugaban Ƙasa bayan ziyartar Kanu a gidan yarin Sakkwato a ranar Lahadi, 30 ga watan Nuwamba, 2025.
“Batun Kanu ne kaɗai aka tattauna, ba a kan harkokin siyasa ba,” in ji Ekeoma.
Ziyarar da Otti ya kai wa Kanu, na zuwa ne bayan da wata Kotun Tarayya a Abuja, ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Ekeoma, ya bayyana cewa ganawar ta shafi batun yadda za a tattauna kan yiwuwar yi wa Kanu afuwa maimakon hukuncin ɗaurin rai da rai da kotu ta yi masa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link