ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aikin Gargaɗi, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta
[ad_1]
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da ta fara.
Ƙungiyar ta kuma bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin wata ɗaya don biyan buƙatunta.
ASUU ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki cikin wa’adin da ta bayar, za ta iya komawa yajin aiki.
ASUU ta fara yajin aikin gargaɗin ne a ranar 13 ga watan Oktoba, 2025.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da suka gudanar a cibiyar ASUU da ke Jami’ar Abuja, inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da nuna halin ko in ka da buƙatun ƙungiyar.
Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025.
Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin.
“Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗi.
[ad_2]
Source link