Benfica ta naɗa Jose Mourinho sabon kociyanta

[ad_1]

Benfica ta sanar da naɗa José Mourinho a matsayin sabon kociyanta, domin maye gurbin Bruno Lage, wanda ƙungiyar ta karo bayan da Qarabag ta doke ta a gasar Zakarun Turai ranar Talata.

Benfica ta kori Lage duk da cewa wasa ɗaya kawai ya yi rashin nasara a dukkanin gasa a bana.

Wata sanarwa da Benfica ta fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa, Mourinho mai shekaru 62 zai jagoranci ƙungiyar har zuwa kakar wasanni ta 2026/2027, tare da zaɓin raba gari a ƙarshen kakar nan.

Tsohon kociyan Chelsea, Real Madrid da Manchester United, ya dawo Benfica ne bayan ya rasa aiki a watan Agusta, wata ɗaya bayan da Fenerbahce ta kore shi sakamakon rashin samun gurbin Gasar Zakarun Turai.

Mourinho ya fara aiki a matsayin koci a Benfica a shekarar 2000, amma ya bar aiki bayan wasanni 11 kacal saboda saɓani da shugabanninta, lamarin da ya ba shi damar koma wa Porto, ƙungiyar da ya daukarwa kofin Zakarun Turai a 2004.

Tun da ya bar Benfica shekaru 25 da suka gabata, Mourinho ya yi aiki da manyan ƙungiyoyi kamar Chelsea, Inter Milan, Real Madrid, Tottenham, Roma da kuma Fenerbahce.

Ya lashe kofin Firimiyar Ingila guda uku, da La Liga, da Serie A, da Champions League guda biyu.

Sai dai daga 2017 zuwa yanzu, babban kambin da ya samu shi ne wanda ya lashe na Gasar Conference League da Roma a shekarar 2022.

A halin yanzu, Benfica tana matsayi na shida a teburin babbar gasar Portugal —Primeira Liga— da tazarar maki biyar tsakaninta da Porto, amma da kwantan wasa ɗaya.

Wasa na farko da Mourinho zai ja ragamar ƙungiyar da ke birnin Lisbon shi ne na ranar Asabar mai zuwa da AVS.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *