’Yan majalisar Amurka sun nemi a sanya wa Kwankwaso da Miyetti Allah takunkumi

[ad_1]



Wasu ’Yan Majalisar Dokokin Amurka guda biyar, sun gabatar da wani ƙudiri da ke neman a sanya wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, tare da ƙungiyoyin Miyetti Allah (MACBAN) da Miyetti Allah Kautal Hore takunkumi.

Takunkuman da ake neman sanya musu sun haɗa da hana su biza da kuma karɓe kadarorinsu.

Ƙudirin “Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026” ’yan majalisa Riley Moore da Chris Smith ne suka jagoranci gabatar da shi.

Ƙudirin ya buƙaci Sakataren Harkokin Wajen Amurka, ya bayar da cikakken rahoto kan ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen kawo ƙarshen kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.

Masu gabatar da ƙudirin sun bayyana cewa ya kamata Amurka ta yi amfani da matsin lambar diflomasiyya, tattalin arziƙi, da tsaro domin tilasta wa Najeriya dakatar da kisan da ake yi wa Kiristoci.

Hakazalika, ƙudirin ya tanadi samar da tallafin jin-ƙai ta hannun ƙungiyoyin sa-kai, tare da duba yiwuwar ayyana wasu ƙungiyoyin makiyaya a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci na ƙasa da ƙasa.

Riley Moore, wanda shi ne ya wallafa ƙudirin, ya jaddada cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya.

Sai dai Gwamnatin Najeriya ta sha musanta irin waɗannan iƙirari, inda ta bayyana cewa matsalolin tsaro a ƙasar suna shafar kowane mutum ba tare da la’akari da addini ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *