EFCC ta shigar da sabuwar tuhuma kan tsohon Akanta-Janar, Ahmed Idris

[ad_1]



Tsohon Akanta-Janar na Najeriya, Ahmed Idris, na fuskantar sabuwar tuhuma daga Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC).

Hukumar na zarginsa da laifuka shida na almundahana, tare da wasu mutum huɗu.

Idris ya riƙe mukamin Akanta-Janar daga 2015 zuwa 2023.

An gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tare da Mohammed Kudu Usman da kasuwar Gezawa Commodity Market and Exchange Limited, kan almundahanar Naira biliyan 109.

Lauyan Idris, Maliki Kuliya Umar, ya bayyana wa kotun cewa wanda yake wakilta bai shirya ba saboda rashin samun wasu takardu da suka shafi shari’ar.

Lauyan ya ce, bisa doka, waɗanda ake zargi sai sun samu isasshen lokaci na kare kansu.

Don haka ya roƙi kotu ta ɗage shari’ar zuwa wani lokaci.

Lauyan wanda ake ƙara na biyu da na uku, Farfesa Nasiru Aliyu SAN, ya goyi bayan bayanin da lauyan Idris ya yi, inda ya ce ya rubuta wasiƙu biyu zuwa ga shugaban EFCC kan yiwuwar warware batun ba tare da zuwa kotu ba.

Lauyan EFCC bai musanta buƙatar lauyoyin ba, amma ya nemi a ba su damar samun takardun da suka ce ba same su ba.

Alƙalin kotu, Yusuf Halilu, ya ce akwai damar yin sulhu tsakanin ɓangarorin biyu.

Kotun ta ɗage shari’ar zuwa 26 ga watan Maris, 2026.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *