Zazzabin Lassa: Mutum 11 sun kamu, wani ya rasu a Gombe
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Gombe ta tabbatar da cewa mutum 11 sun kamu da cutar zazzabin Lassa, yayin da wani mutum ɗaya ya rasu.
Gwamnatin ta bayyana cewa cutar ta samo asali ne daga Jihar Taraba, amma daga baya ta yaɗu zuwa Gombe.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Gombe, Dokta Habu ne, ya bayyana hakan yayin wani taro kan ɓarkewar cututtuka da aka gudanar a jihar.
Ya ce wanda ya rasu fara nuna alamun cutar ne a Taraba kafin daga bisani aka kai shi Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe.
“Duk da cewa an kula da marasa lafiyar a Gombe, asalin cutar daga Taraba ta fito,” in ji Dokta Habu.
Ya ƙara da cewa yawancin waɗanda suka kamu da cutar na daga cikin mutanen da ke zuwa Taraba domin aikin noma.
Ya jaddada cewa ko mutum ɗaya ne ya kamu da cutar, gwamnatin jihar na daukar lamarin da girma saboda hatsarin cutar.
Kwamishinan ya ce Gwamnatin Gombe ta ɗauki matakan kariya tun da wuri, ciki har da tanadin magunguna da kayan aiki, tare da haɗin gwiwa da hukumomi kamar NCDC, WHO da UNICEF, domin daƙile yaɗuwar cutar.
A ƙarshe, ya buƙaci jama’a da hukumomi da su riƙa gano cututtuka da wuri, tare da bayar da rahoto cikin gaggawa.
Ya buƙaci a ƙarfafa haɗin kai tsakanin jihohi domin hana yaɗuwar zazzabin Lassa da sauran cututtuka masu yaɗuwa a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link