’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 3 da mutum 5 a Taraba

[ad_1]



Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe ’yan sanda uku da wasu mutum biyar a Jihar Taraba.

Harin ya faru ne a yankin Tor-Damisa, da ke Ƙaramar Hukumar Donga, inda maharan suka shiga yankin suka fara harbe-harbe.

Mutane da dama sun tsere zuwa cikin dazuka domin tsira da rayukansu.

’Yan sanda sun ce sun samu kiran gaggawa, sannan suka tura jami’ai tare da sojoji zuwa wajen.

An yi musayar wuta, kuma jami’an tsaro sun fatattaki maharan.

Kakakin ’yan sandan jihar, ya ce jami’ai uku sun rasa rayukansu a lokacin harin, yayin da wasu suka jikkata.

“Sun zo da yawa suka fara harbi. Mutane suka dinga gudu ta ko ina. Gaba ɗaya al’umma ta shiga cikin firgici,” in ji wani mazaunin yankin.

’Yan sanda sun kuma nuna alhininsu kan waɗanda aka kashe, tare da jajanta wa iyalansu.

Har yanzu jami’an tsaro na yankin domin tabbatar da zaman lafiya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *