Yadda Messi Ya Jefa Kwallaye 900 A Tarihinsa Na Kwallon Kafa

[ad_1]

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina Lionel Messi ya zura kwallo ta 900 a tarihinsa na kwallon kafa a ranar Laraba, a wasan da Inter Miami ta buga canjaras da Nashville Fc a gasar CONCACAF, Messi mai shekaru 38, ya zura kwallo mai ban mamaki bayan mintuna bakwai kacal da fara wasan.

Kwallon da dan wasan na Argentina ya ci itace ta 81 da ya ci tun bayan komawarsa Inter Miami daga PSG a shekarar 2023, Lionel Messi wanda ya lashe kyautar Ballon D’Or sau takwas a baya ya zura kwallaye 672 a zaman da yayi a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona yayinda ya zura 32 ga Paris Saint-Germain ta Faransa, da kuma karin kwallaye 115 da yaci a matakin kasa da kasa da kasa ga kasar Argentina.

  • ADC Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Saki El-Rufai Ko Ta Gurfanar Da Shi A Kotu
  • Yadda Kasar Sin Ke Tabbatar Da Babban Burinta A Aikace

Shekaru 21 da fara taka leda a matsayin matashin dan kwallo Messi ya buga wasanni fiye da 1000 a kungiyoyi 3 da ya zauna, wasan da Messi ya fara bugawa shine wanda Barcelona ta doke Albacete da ci 2-0 a shekarar 2005 a matsayin matashin dan wasa mai shekaru 17, duk da cewa har yanzu akwai kwallaye 65 tsakaninsa da babban abokin hamayyarshi Cristiano Ronaldo amma a matsayinsa na dan wasan tsakiya ana kallon wannan a matsayin abin burgewa.

Ana sa ran Messi zai buga gasar cin kofin duniya na shida a wannan shekarar, lokacin da Argentina za ta kare kambunta a gasar ta bana wadda kasashe 48 za su fafata a kasashen Amurka, Kanada da Mexico, tauraron dan wasan na Argentina ya riga ya tsawaita kwantiraginsa a Inter Miami har zuwa karshen kakar wasa ta shekarar 2028.

Messi ya zura kwallaye 672 a wasanni 778 da ya buga a tsawon shekaru 17 da ya shafe a Spain, a zaman da yayi a kungiyar PSG ta kasar Faransa, ya zura kwallaye 32 a wasanni 75, inda ya lashe kofuna uku ciki har da kofuna biyu na lig, a Inter Miami kuwa, kwallaye 81 da ya ci sun zo ne a wasanni 96 kacal, wanda ya taimaka wa kungiyar lashe Kofin League a shekarar 2023 da kuma kofin MLS na shekarar 2025, hakazalika ya zura kwallaye 115 a matakin kasa da kasa a wasanni 196, ciki har da kwallo biyu da ya zura a wasan karshe na Kofin Duniya na shekarar 2022 da aka buga a kasar Qatar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *