Yadda Kasar Sin Ke Tabbatar Da Babban Burinta A Aikace
[ad_1]
Kwanan nan, batun “yaya za a tantance nasarorin gwamnati” ya zama batu da ake yawan ambato a nan kasar Sin. Sinawa suna ta tofa albarkacin bakinsu a kan mene ne ainihin ma’anar “nasarorin gwamnati”?
A kasar Sin, ma’aunin nasarorin gwamnati ba shi ne yadda aka furta maganganun fatar baka ba, sai dai ko an warware matsaloli.
A lokacin zafi na shekarar 2017, Huang Ying, wacce ke rike da mukamin “shugabar kogi” watau mai kula da harkokin kogi a gundumar Qingshen da ke kogin Minjiang a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, ta kan fara aikin kowace rana da duba kogin, inda ta kan tsuguna ta shafa ciyayin cikin ruwa don tantance ingancin ruwa, sannan ta duba kowace magudanar fitar da gurbataccen ruwa da ke bakin kogin. Ba ita kadai ce ta yi wannan fafutukar ba, “shugabannin kogi” sama da miliyan 1.2 a duk fadin kasar wadanda suka fara tun daga kan shugabannin larduna har zuwa jami’an kauyuka, sun mai da babban burin “kare koguna” ya zama wasu hakikanan ayyuka kamar su “duba kogi sau daya a ko wace rana” da “tabbatar da kowace magudanar fitar da gurbataccen ruwa ta cika ma’auni”. A yanzu haka, sashen kogin Minjiang da Huang Ying ke kula da shi ba wai kawai ya kara tsabta ba, har ma an gina hanyar koren gandun daji na itatuwan gora mai tsawon kilomita 40, matakin da ya sa ya zama wurin shakatawa da jin dadin rayuwa ga mazauna wurin, kuma yana samar da kudin shiga yuan biliyan 1.6 a ko wace shekara a bangaren yawon shakatawa na al’adu. A hakika, ba a rasa samun irin labarai a kasar Sin ba.
A takaice dai, a kasar Sin, nasarorin gwamnati ba su ne rahotanni a ofisoshi ba, a maimakon haka, sun kasance canje-canje da ke faruwa ga rayuwar jama’a, ciki har da sauya ruwan kogi daga mai datti zuwa mai tsabta, da fitowar tsirrai a cikin hamada, da kuma kara samun wadata a kauyukan da ke fama da talauci… Jama’ar kasar Sin suna bayyana ainihin “nasarorin gwamnati” ta hanyar gudanar da ayyukansu na zahiri, wanda hakan kuma ya shaida sirrin jam’iyya mai mulki a kasar wajen jagorantar jama’ar kasar don tabbatar da babban burin da ake son cimmawa. (Mai fassara Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link