Hisbah Ta Kama Mutane 21 A Otel A Kano
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mutum 21 a wani otel a Kureken Sani, Kumbotso. An kama su ne bisa zargin aikata aiyukan da suka saɓa dokokin Hisbah.
Mataimakin Babban Kwamanda, Dr. Mujahid Aminuddeen, ya tabbatar da kama su ga manema labarai. Ya ce cikin su akwai mata 11, wasu na tsakanin shekaru 17 zuwa 25.
- Hisbah Ta Kano Ta Kama Matasa 583 Bisa Zargin Rashin Ɗa’a A Lokacin Sallah
- Hisbah Ta Kama Wasu Matasa 9 Kan Shirya Casun Bankwana Da Shaiɗan A Kano
Ya ƙara da cewa maza 10 ne aka kama, yawancinsu matasa ƙasa da shekara 30. An kama su ne yayin wani taro da ake zargin ya saɓa ƙa’idojin Hisbah.
Haka kuma an kama manajan otel ɗin da ake zargi da hannu a lamarin. Hukumar ta ce za a gurfanar da dukkan waɗanda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar hukunci.
Sheikh Aminuddeen ya buƙaci jama’a su kasance masu sa ido kan irin waɗannan aiyuka. Wannan na zuwa kwanaki bayan kama matasa sama da 600 a lokacin bukukuwan Sallah.