Sin Ta Nemi Kasashen Duniya Su Hada Kai Wajen Magance Matsalolin Ilimin Yara A Yankunan Da Ake Fama Da Rikici
[ad_1]
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong ya yi jawabi a wajen wani taron jama’a na kwamitin sulhu na MDD a ranar 2 ga watan nan, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai wajen magance matsalar ilimi da yara ke fuskanta a yankunan da ake fama da rikici.
Ya yi Allah wadai da cin zarafin kananan yara, kana ya yi kira da a tsagaita bude wuta, da hawa teburin tattaunawa don warware sabani, sannan ya bukaci kwamitin sulhun da ya sauke nauyin da ke wuyansa. Ya kuma yi kira ga Isra’ila da ta yi aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da dage takunkumin hana kai kayan agaji yankin Gaza.
Kazalika, Fu Cong ya bayyana cewa, ya kamata a kara zuba jari a fannin ilimi, sannan a yi amfani da fasaha wajen tallafa wa ilimi. Kasar Sin tana son yin aiki tare da kasashen duniya wajen kare hakkoki da muradun yara a yankunan da ake fama da rikici. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link