Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung
[ad_1]
Da yammacin yau Asabar bisa agogon wurin, shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae-myung ya tattauna da shugaban Sin Xi Jinping a Gyeongju na Koriya ta Kudu.
Yayin tattaunawar, Xi Jinping ya bayyana cewa inganta ci gaban dangantaka tsakanin Sin da Koriya ta Kudu ya kasance zabi mai kyau wanda ya dace da muradun al’ummomin biyu da kuma ci gaban zamani. Ya gabatar da shawarwari guda hudu don bude sabon babi a dangantakar Sin da Koriya ta Kudu, ta farko, karfafa mu’amala kan tsare-tsare, ta biyu, zurfafa hadin gwiwa mai amfani ga juna, ta uku, karfafa huldar dake tsakanin al’ummun kasashen biyu, ta hudu kuma, karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban.
A nasa bangare, Lee Jae-myung ya bayyana cewa, Koriya ta Kudu tana mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin kuma tana son yin aiki tare da kasar Sin don inganta ci gaban huldar abokantaka da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin nasara a shekara mai zuwa.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link