Kotu Ta Janye Tuhume-tuhumen Da Ake Yi Wa Sanata Natasha

[ad_1]

Wata Babbar Kotu da ke Abuja ta janye dukkanin tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya ta shigar a kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.

Gwamnatin ta janye ƙarar ne bayan ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya shigar da takardar dakatar da ƙarar.

  • Zargin Almundahanar ₦1.35bn: Kotun Ƙoli Za Ta Warware Taƙaddamar EFCC Da Lamiɗo
  • Gwamnatin Kaduna Ta Ce Shari’ar Zidan Ta Gudana Cikin Gaskiya da Adalci

An danganta shari’ar da wasu kalamai da ake zargin Sanatan ta yi a wata hira a gidan talabijin.

Alƙalin kotun Mai shari’a, Justice C. N. Oji, ya amince da janye ƙarar, inda ya ce hakan na nuna buƙatar yin taka-tsantsan wajen amfani da ikon gurfanarwa.

Bayan hukuncin, Sanata Akpoti-Uduaghan ta ce wannan mataki ya wanke ta, tare da jaddada ƙudirinta na ci gaba da yi wa al’ummarta hidima da kare dimokuraɗiyya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *