Lafiyata garau, ba jinya ta kai ni London ba — Akpabio
[ad_1]
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana fama da rashin lafiya mai tsanani.
Akpabio, wanda ya sauka a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin, bayan dawowa daga London, ya samu tarba daga wasu sanatoci, hadimai da magoya baya.
Dawowarsa na zuwa ne bayan yada jita-jita a kafafen sada zumunta cewa yana kwance a asibiti a London.
Da yake magana da ’yan jarida a filin jirgin, Akpabio ya bayyana rahotannin da ke yawo a matsayin karya da marasa tushe.
“Babu wani abu makamancin haka. Lafiyata kalau. Na tsaya ne don yin hutun gajeren lokaci a London,” in ji shi.
Kafin zuwansa London, Akpabio ya halarci taron shugabannin majalisun dokoki na duniya karo na shida da aka gudanar a birnin Geneva na aksar Switzerland, daga ranar 29 zuwa 31 ga watan Yuli.
Ya bayyana cewa tawagar Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta dimokuradiyya da hadin gwiwa tsakanin bangarorin gwamnati.
Akpabio ya kuma yi alkawarin cewa Majalisar Dattawa za ta dawo da muhimman ayyukan dokoki da suka shafi ci gaban kasa bayan hutun majalisa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link