An buga wa matashi ƙusa a ka kan zargin satar kaza a Zariya

[ad_1]



Wasu ’yan bijilanti sun cika wandonsu da iska bayan an zarge su da buga wa wani matashi mai shekara 20 ƙusa a kan shi a Zariya, saboda zarginsa da satar kaza.

Mahaifin yaron, mazaunin unguwar Limancin Kona, ya bayyana wa Aminiya cewa, ya aiki yaron ne da kazarsa domin ya siyar a kasuwa, inda su kuma ’yan bijilantin suka kama shi suka kai shi ofishinsu, bisa zargin sato kazar ya yi.

Mahaifin matashin Mallam Salisu Nuhu, wanda aka fi sani da Babande, ya ce bayan karɓo yaron a hannunsu ne ya lura da raunin da ke kansa, na ƙusa mai tsawon inci biyar.

Babande, wanda ke sana’ar gyaran mota, ya ce, “Sun tsare shi, suka azabtar da shi har suka buga masa ƙusa mai tsawon inci biyar a kansa.”

Ya ƙara da cewa daga baya an kira shi zuwa ofishin ’yan sa-kai na Anguwar Sirdi, inda aka nemi ya biya naira dubu biyar a matsayin belin ɗansa.

Saboda rashin kuɗi, aka ce ya tafi da ɗansa gida ya dawo da kuɗin kashegari.

A gida ne Babande ya gano raunuka a kan ɗansa, inda Aliyu ya bayyana masa cewa wani ɗan sa-kai mai suna Nuhu Dan Banga ne ya buga masa ƙusa a kai yayin azabtar da shi.

Daga nan aka kai shi wani kyamis mai zaman kansa, wanda ya tura su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) Shika saboda tsananin raunin.

Babande ya ce sun kashe fiye da naira dubu dari takwas wajen magani bayan an yi wa ɗan nasa tiyata don cire ƙusar da ta zauna a kansa har tsawon kwanaki 13.

Aliyu ya ce: “Na roƙe su su kira mahaifina don tabbatar da cewa kazar tasa ce, amma suka ƙi. Na suma lokacin da Nuhu Dan Banga ya soka ƙusar a kansa.”

Kwamandan ’yan sanda na cikin garin Zariya, Nura Abubakar, ya tabbatar da kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, yayin da ɗayan ya tsere.

Ya tabbatar da cewa da zarar an kama shi za a gurfanar da su a kotu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *