Ni Da Tinubu Mun Yi Hannun Riga Kuma Ba Za Mu Taɓa Zama Waje Ɗaya Ba – El-Rufai
[ad_1]
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce bai taɓa samun kusanci na siyasa da Shugaba Bola Tinubu ba.
Da yake magana a Trust TV, El-Rufai ya ce mutane da dama suna tunanin suna da alaƙa mai ƙarfi, amma a cewarsa hakan ba gaskiya ba ne.
- Ministocin Wajen Sin Da Nijeriya Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Diflomasiyya
- Kamfanin Matatar Man Fetur Na Dangote Ya Rage Farashin Mai Zuwa ₦774
Ya bayyana cewa ya goyi bayan takarar Tinubu a zaɓen 2023 ne bisa ƙa’idojin jam’iyya, ba don wata alaƙa ta musamman a tsakaninsu ba.
A cewarsa, akwai yarjejeniya a cikin jam’iyyar APC cewa bayan shekaru takwas na mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, mulki zai koma Kudu.
Da Tinubu ya zama ɗan takarar jam’iyyar, ya yi iya ƙoƙarinsa domin APC ta yi nasara a zaɓen.
Sai dai El-Rufai ya ce daga baya sun gano cewa suna da manyan bambance-bambance a ɗabi’u da salon mulki.
Ya ce shi a ganinsa, aikin gwamnati na nufin kawo sakamako da ci gaba, ba buƙatar ƙashin kai ba.
Ya ƙara da cewa ko da an naɗa shi minista a gwamnatin Tinubu, da ba zai daɗe ba saboda saɓanin aƙida da salon shugabanci.
“Mu layuka ne da ba za su taɓa haɗuwa ba,” in ji El-Rufai, yana mai jaddada cewa ba su da manufa ko aƙida iri ɗaya.
[ad_2]
Source link