Adadin Kamfanonin AI Na Sin A Shekarar 2025 Ya Haura 6,000

[ad_1]

Adadin kamfanonin kirkirarriyar basira ta AI dake kasar Sin a shekarar 2025 ya haura 6,000, yayin da ake hasashen fadadar darajar masana’antun kasar masu dogaro da fasahohin AI na iya kaiwa sama da yuan tiriliyan 1.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 171.39 a shekarar ta 2025.

Game da hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Laraba, mataimakin ministan ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin Zhang Yunming, ya ce, a shekarar ta 2025, kamfanonin cikin gida na Sin sun fitar da kayayyakin hada laturori daban daban masu kunshe da fasahohin AI, yayin da mizanin awon karfin kirkirarriyar basira na kamfanonin kasar Sin ya kai EFLOPS 1,590. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *