Jakadan Sin a Najeriya Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Aikin Cibiyar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Najeriya

[ad_1]

An gudanar da bikin kaddamar da aikin cibiyar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Najeriya a jiya Litinin, aikin da asusun raya duniya da hadin gwiwar kasashe masu tasowa na (GDSF) ya tallafawa, kuma hukumar bunkasa masana’antu ta MDD (UNIDO) ta aiwatar da shi.

Jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai, da wakilin hukumar UNIDO a Najeriya, da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) Johnson Philbert Abaka, da wakilan ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli ta tarayyar Najeriya, da wakilin ma’aikatar kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha ta tarayyar, da shugaban jami’ar Abuja Hakeem Babatunde Fawehinmi da sauransu sun halarci bikin.

Yayin bikin, jakada Yu Dunhai ya bayyana cewa, aikin cibiyar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa, wani takamaiman mataki ne na aiwatar da shirye-shiryen taron koli na Beijing, na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC). Ya ce aiki na daya daga cikin abubuwa masu alamta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da MDD, a karkashin tsarin shawarar ci gaban duniya da Sin ta gabatar.

Daga nan sai ya yi fatan dukkan bangarorin za su karfafa hadin gwiwa, da inganta karfin cibiyar, da kuma taimakawa kasashen Afirka wajen karfafa ikon samarwa da farfado da makamashi, duk da kalubale, ko mawuyancin halin da ake ciki, da kuma samun ingantaccen ci gaba mai dorewa. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *