Netanyahu ya ba da umarnin kai mummunan farmaki a Gaza
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya umarci rundunar sojin ƙasar da ta kai mummunan farmaki a Zirin Gaza, bayan ya zargi ƙungiyar Hamas da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
Wata sanarwa da ofishin firaministan ya fitar, ta ce: “Bayan tattaunawar tsaro, Firaminista Netanyahu ya umurci rundunar soji da ta gaggauta kai hare-hare masu ƙarfi a Zirin Gaza.”
Sanarwar na zuwa ne bayan Isra’ila ta zargi Hamas ta karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma kwanakin baya domin ba da damar kai agaji ga fararen hula da ke yankin.
Tun da farko dai Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani kan abin da ya kira saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta, inda ya ce Hamas ta gaza tabbatar da sharuɗɗan yarjejeniyar da suka haɗa da miƙa dukkan mutanen da ta yi garkuwa da su waɗanda suka haɗa rayayyu da matattu.
Duk da gwamnatin Isra’ila ta tabbatar da cewa ƙungiyar Hamas ta miƙa waɗanda suka raye, amma har yanzu ba ta ƙarasa miƙa gawarwakin matattun ba, abin da ya janyo zargin cewa tana ƙoƙarin saɓa yarjejeniyar.
A nata ɓangaren kuwa, Hamas ta bayyana cewa nemo gawarwakin na da wahalar gaske ne, saboda baraguzan gine-ginen da Isra’ila ta rusa da ke kawo cikas wajen lalubo gawarwakin.
A bayan nan ne Isra’ila ta tabbatar da cewa gawar mutumin da Hamas ta miƙa mata a ranar Litinin ba ta cikin gawarwakin da ƙungiyar ta yi garkuwa da su da aka tsara za ta mayar da su.
Har yanzu dai ana neman gawarwaki 13 daga cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su, waɗanda ake tunanin za ta miƙa domin cika sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da Shugaba Trump ya tsara domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Hukumomin Isra’ila sun ɗauki hakan a matsayin yunƙurin Hamas na karya alƙawarin da aka shiga domin kawo ƙarshen yaƙin.
Mun jinkirta miƙa gawa a yau Talata —Hamas
Ƙungiyar Hamas ta sanar da cewa ta jinkirta miƙa gawar wani wanda aka tsara za ta miƙa da yammacin Talatar nan, saboda abin da ta kira saƙonin karya yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi.
A sanarwar da sashen yaƙin ƙungiyar, Ezzedine Al-Qassam Brigades, suka fitar, ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin “saɓa yarjejeniyar tsagaita tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani wajen tsara ta.”
“Za mu jinkirta miƙa gawar da aka tsara a yau (Talata) saboda take haƙƙin da Isra’ila ta yi.
Duk wani sabon farmaki daga Isra’ila zai iya kawo cikas wajen aikin bincike, tono, da ceto gawarwakin,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta fito ne ‘yan mintuna kaɗan bayan Firaminista Netanyahu ya umurci sojojinsa da su kai mummunan farmaki a Zirin Gaza, yana zargin Hamas da karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta.