’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi
[ad_1]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wasu mutum huɗu a yankin Kamba da ke jihar, bisa zargin su da shigar da babura uku da suka saya daga Jamhuriyar Benin domin kai wa kungiyar ta’addanci ta Lakurawa.
Haka kuma an kama wani Mubarak Ladan bayan ya yi tayin cin hancin naira dubu dari shida (₦600,000) ga DPO na Kamba, SP Bello Mohammad Lawal, domin a saki waɗanda aka kama.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce baburan da ake kira “Boko Haram” guda uku an saye su ne kan kudi naira miliyan 5 da dubu 400, kuma an tanadar da su ne domin kai wa kungiyar Lakurawa ta hannun wani Alhaji da ke a Kangiwa.
Sanarwar ta ƙara da cewa an cafke mutanen ne bayan samun sahihan bayanai, inda jami’an ’yan sanda tare da ’yan sa-kai ƙarƙashin jagorancin DPO na Kamba suka kai samame
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi, Bello M. Sani, ya umurci Mataimakin Kwamishina na Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID), Birnin Kebbi, da ya bi sahun sauran waɗanda suka tsere a lamarin
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link