Ghana ta kama mutum 141 kan zargin aikata damafara a Intanet

[ad_1]



Hukumomin tsaro a ƙasar Ghana sun kama mutum 141 da ake zargi da aikata damfara a intanet a safiyar ranar Asabar.

An kama mutanen ne a wani samame da aka kai unguwannin Tabora da Lashibi da ke birnin Accra.

Yawancin waɗanda aka kama ’yan Najeriya ne.

Hukumomin sun ce sun kai samamen ne domin daƙile ayyukan ƙungiyoyin da ke aikata damfara ta intanet da sauran laifuka.

An kuma kama wani ɗan ƙasar Ghana da ake zargi da bai wa mutanen da aka kama masauki.

A yayin samamen, jami’an tsaro sun ƙwato kwamfuta 38 da wayoyin salula 150 da ake amfani da su wajen aikata damfara a intanet.

Ministan sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da fasaha na Ghana, Sam George, ya ce ana zargin mutanen da aikata laifuka daban-daban na zamba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Sam George ya ce ana ci gaba da binciken kayan da aka ƙwato, kuma duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi bisa dokokin ƙasar Ghana.

Wannan samame ya biyo bayan kama wasu mutum 48 da aka yi a ranar Laraba, lamarin da ke nuna yadda Ghana ke ƙoƙarin yaƙar ayyukan masu zambar intanet.

Wani rahoto da hukumar ’yans andan duniya ta Interpol ta fitar a shekarar 2025 ya nuna cewa laifukan zamba na ƙara ƙaruwa a nahiyar Afirka.

A baya-bayan nan, Ghana ta kori wasu masu zamba da suka damfari sama da mutum 200 kuɗin da ya kai dala 400,000, inda ake zargin suna gudanar da ayyukansu ne tsakanin Ghana da Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *