Majalisar Dokokin Kasar Sin Za Ta Gudanar Da Taron Shekara-shekara A Ranar 5 Ga Watan Maris

[ad_1]

A ranar 5 ga watan Maris ta shekarar 2026 ce za a bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 (NPC) a nan birnin Beijing, bisa shawarar da zaunannen kwamitin NPC ya yanke a yau Asabar.

An yanke shawarar ce a karshen zaman taro na zaunannen kwamitin NPC da aka gudanar daga ranar Litinin zuwa Asabar.

Ajandar taron shekara-shekara na NPC da aka ba da shawara a kai ta kunshi yin nazari da tattaunawa kan rahoton ayyukan gwamnati, da bitar daftarin shirin shekaru biyar-biyar karo na 15 (daga shekarar 2026 zuwa ta 2030) na bunkasa raya kasa da zamantakewar al’umma, da nazarin rahoton aiwatar da shirin shekara-shekara kan ci gaban tattalin arzikin kasa da habaka zamantakewar al’umma na shekarar 2025, da kuma daftarin shirin raya tattalin arziki da zamantakewa na kasa na shekarar 2026.

A bisa taron kwanan baya da ka gudanar na shugabannin kwamitin kasa na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC) na 14, an ba da shawarar fara zaman taro na hudu na CPPCC na 14 a ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2026, a nan birnin Beijing. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *