Ramadan: Coci Ta Raba Kayan Abinci Ga Makarantun Tsangaya A Kaduna
[ad_1]
Cocin Evangelica da ke Sabon Tasha, Kaduna, ta raba buhunhunan shinkafa, masara da sauran kayan abinci ga Musulmai, makarantun Islamiyya na Tsangaya da kuma wasu mutane da suka rasa matsugunansu (IDPs), kafin azumin Ramadana.
Babban Limamin cocin, Yohanna Buru, wanda ya jagoranci rabon kayan a masallacin Kano Road da ke Kaduna, ya ce; an yi hakan ne domin inganta zaman lafiya da kuma karfafa jituwa a tsakanin addinai daban-daban a fadin jihar.
- Neymar Na Duba Yiwuwar Ritaya Daga Ƙwallon Ƙafa A Ƙarshen Shekara
- Sin Ta Ba Da Shawarar Tsayawa Kan Ra’ayoyin Bai Daya Guda Biyar Don Warware Rikicin Sudan
Buru ya ce, cocin kusan tsawon shekaru 20 da suka gabata, ta tallafa wa Musulmai marasa galihu da makarantun Tsangaya a jihohi biyar na Arewa da kayayyakin abinci, domin ba su damar gudanar da azumin watan Ramadana na kwana 30 a cikin sauki.
Ya kara da cewa, baya ga shinkafa da masara, cocin tana kuma samar da tabarmun sallah da butoci a kowace shekara, inda yake kira ga wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da lokacin wajen addu’ar neman zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma kawo karshen rashin tsaro da wahalhalun tattalin arziki a kasar.
“Yayin da farashin kayayyaki ke ci gaba da hauhawa, mun tattara fastoci da limamai kimanin 50 masu aikin sa kai, domin yin wani gangamin wayar da kan jama’a na tsawon kwana bakwai, don karfafa ‘yan kasuwa su rage farashin kayayyakin abinci a lokacin na Ramadana,” in ji shi.
Ya kara da cewa, cocin yana kuma taimakawa wajen fitar da wasu fursunoni Musulmai a kowace shekara, domin ba su damar yin azumin Ramadana tare da iyalansu.
Haka zalika, Buru ya yaba da goyon bayan wata mai taimakon jama’a Musulmai, Hajiya Ramatu Tijjani, wacce ke ba da gudummawa ga zawarawa da marayu a lokacin bukukuwan kirsimeti da dabuwar shekara, yana mai bayyana wannan a matsayin nuna girmamawa tsakanin addinai.
Ya yi wa Musulmai fatan alheri a watan Ramadana mai cike da zaman lafiya, sannan kuma ya yi kira da a yi addu’o’i don, hadin kai a kasar baki-daya.
A cikin jawabinsa, shugaban kungiyar nakasassu a Jihar Kaduna, Mallam Hassan Lawal, ya yaba wa cocin bisa wannan tallafi, yana mai kira ga sauran Musulmai masu hannu da shuni, da su taimaki marasa galihu a wannan lokaci na Azumi.
[ad_2]
Source link