Ɗaliban Nijeriya Sun Nemi A Dakatar Da Dokor Haraji
[ad_1]
Ƙungiyar Ɗaliban ta ƙasa (NANS) ta nuna damuwa matuƙa kan shirin aiwatar da sabbin dokokin haraji da aka tsara su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026. Ƙungiyar ta ce duk da amincewa da muhimmancin gyaran haraji wajen ƙarfafa kuɗaɗen shiga da tattalin arziƙi, hanyar aiwatar da dokokin ba su da inganci kuma ba a yi cikakken bayani ga jama’a ba.
A wata sanarwa da Shugaban NANS na Ƙasa, Kwamared Olushola Oladoja, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta yi gargaɗi cewa aiwatar da dokokin a halin da ake ciki na iya ƙara ƙuncin rayuwa da rashin amincewa tsakanin jama’a da gwamnati. Ta ce ƴan Nijeriya ba su da cikakkiyar masaniya kan abun da dokokin suka ƙunsa da tasirinsu na dogon lokaci.
- An Sanar Da Kananan Dandaloli Hudu Na Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na 2026 Na CMG
- An Wallafa Littafin “Bayanai Kan Jerin Tunanin Tattalin Arziki Na Xi Jinping”
NANS ta ƙara da cewa akwai fargaba a faɗin ƙasar nan cewa dokokin za su ƙara wa jama’a nauyin rayuwa, tare da raunana kasuwanci da shirye-shiryen kuɗi, musamman ganin halin matsin tattalin arziƙi da ake ciki.
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda aka yi watsi da manyan ƙungiyoyin matasa da na ɗalibai kamar NANS da NYCN wajen wayar da kai, duk da irin yawan mambobinsu da tasirinsu a ƙasa.
Saboda haka, NANS ta nemi a dakatar da aiwatar da dokokin har sai an gudanar da cikakken wayar da kai a duk faɗin ƙasa, tare da neman Majalisar Tarayya ta kammala bincikenta kan zargin sauye-sauyen da aka yi wa dokokin. Ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin kwanaki 14 ba, za ta shirya zanga-zangar ƙasa baki ɗaya.
[ad_2]
Source link