Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 5, Sun Ceto Yara 3 A Borno Da Yobe
[ad_1]
Sojojin rundunar Operation HADIN KAI sun kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne guda biyar, sannan sun ceto yara uku da aka sace a hare-haren daban-daban da suka gudanar a Jihohin Borno da Yobe.
A cewar rundunar, an gudanar da ayyukan ne tsakanin ranakun 20 zuwa 21 ga watan Fabrairu.
- Bakar Inuwa, Gwamma Rana Da Ke
- Ƴan Gudun Hijira 43,000 Sun Amfana da Tallafin Gwamnatin Sakkwato
Sojoji sun yi artabu da mayaƙan ISWAP a wani a kusa da ƙauyen Sabsawa a Jihar Borno, inda suka kashe biyar daga cikinsu, sauran kuma suka tsere.
A wani samame daban da aka kai ƙauyen Ngurosoye da ke ƙaramar hukumar Bama a Jihar Borno, sojoji sun ceto yara uku; Abba Abba, Fatima Abba da Aisha Abba.
Rahotanni sun nuna an sace su kimanin watanni biyu da suka wuce a hanyar Gubio kafin daga bisani a kai su Bula-Daloye.
An miƙa yaran ga ‘yansanda domin ci gaba da bincike.
Haka kuma, rundunar ta ce wani matashi mai shekaru 18 ya miƙa wuya a Geidam, Jihar Yobe, kuma yana hannun jami’an tsaro domin tantancewa.
Rundunar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da ayyukan sintiri da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin tsaron al’umma domin rage hare-haren ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.
[ad_2]
Source link