Ramadan: Gwamnan Yobe ya bai wa ma’aikata tallafin kayan abinci
[ad_1]
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayar da tallafin kayan abinci ga ma’aikatan ƙwadago domin su samu abin da za su ci yayin gudanar da azumin watan Ramadan.
Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Abubuwan Hawa ta Jihar Yobe (YOROTA), Alhaji Babagana Modu Bature Goniri ne, ya jagoranci rabon tallafin ga waɗanda suka amfana.
Da yake jawabi a wajen rabon tallafin, ya bayyana cewa shirin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na rage wa al’umma raɗaɗin rayuwa, musamman masu ƙaramin ƙarfi, domin su gudanar da azumi cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Ya kuma yaba wa gwamna Buni kan yadda yake ci gaba da nuna kulawa ga walwalar jama’a, yana mai cewa irin wannan tallafi na ƙara ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin al’umma.
Haka kuma, ya yi kira ga waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya dace.
Babagana Modu ya yi addu’ar Allah Ya karɓi ibadun al’umma, Ya wanzar da zaman lafiya da ci gaba ga Jihar Yobe da ƙasa baki ɗaya.
Wani daga cikin waɗanda suka amfana, Malam Bukar, ya ce tallafin ya zo a daidai lokacin da ya dace, domin a cewarsa bai tanadi komai ba don azumin Ramadan.
Shi ma wani lebura mai suna Malam Usman, ya bayyana jin daɗinsa game da tallafin.
“Na ji daɗin wannan tallafi matuƙa, domin a yanzu ba ni da abin da zan ci yau balle na gobe, gashi kuma an fara azumi.
“Wannan zai taimaka ƙwarai wajen inganta rayuwata da ta iyalina. Muna godiya da wannan karamci.”
Ga hotunan yadda rabon ya gudana:
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link