Ɗan ƙunar baƙin wake ya ta da bam a masallaci a Maiduguri

[ad_1]



Mutane da dama sun rasu yayin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya ta da bam a wani Masallacin da ke yankin Gambarou Jumu’at a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.

Wasu daga cikin masu masallata da suka tsira, sun ce ɗan ƙunar baƙin waken, ya shiga masallacin ne a ɓoye, sannan ya tayar da bam ɗin ne a lokacin da ake tsaka da sallar Magariba.

“Ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam ne a raka’a ta farko lokacin da ake yin sallar Magariba.

“Mutane da dama sun rasu, yayin da wasu suka jikkata,” in ji ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira.

Har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

Sai dai ana zargin ƙungiyar Boko Haram, wadda ta sha kai hare-haren ƙunar baƙin wake a yankin cikin watannin baya.

Karin bayani na tafe…


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *