Xi Jinping Ya Zanta Da Donald Trump Ta Wayar Tarho
[ad_1]
A daren jiya 4 ga watan Fabrairu, shugaban kasar Sin Xi Jinping zanta da takwaransa na Amurka Donald Trump ta wayar tarho.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, bangarorin biyu sun ci gaba da samun kyakkyawar mu’ammala. Yana matukar darajata dangantakar Sin da Amurka. A sabuwar shekarar da ake ciki, yana fatan ci gaba da karfafa dangantakarsu da samun bunkasa ba tare da tangarda ba. Ya ce, kasashen biyu za su iya samun hanyar magance abubuwan dake jan hankulansu, muddin bangarorin biyu suka rike matsayin daidaito da mutunta juna tare da hadin gwiwa da cin moriya tare. Ya kamata bangarorin biyu su bi yarjejeniyar da suka cimma, su karfafa tattaunawa da tuntubar juna, kuma su daidaita sabanin ra’ayi yadda ya kamata, kana da fadada hadin gwiwa tsakaninsu, tare da kara amincewa da juna, da bin hanyar da ta dace, ta yadda za a iya sanya shekarar 2026 ta zama shekarar mutunta juna da zaman lafiya tare da hadin gwiwa, ga Sin da Amurka.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, batun Taiwan shi ne batu mafi muhimmanci a cikin dangantakar Sin da Amurka. Taiwan yanki ne na Sin, kuma dole ne bangaren Sin ya kare ikon mallakar kasa da cikakken yankinta, ba zai yiwu ko kadan bangaren Sin ya amince a ware Taiwan daga yankinsa ba. Ya zama dole ga bangaren Amurka ya yi taka-tsantsan kan batun sayar da makamai ga yankin Taiwan.
A nasa bangare, Trump ya bayyana cewa, Amurka da Sin manyan kasashe ne, kuma dangantakarsu ta fi muhimmanci a duk duniya. A cewarsa, yana da babbar alaka da shugaba Xi, kuma yana matukar girmama da mutunta shugaba Xi.
Donald Trump ya kara da cewa, bisa jagorancinsa da na Shugaba Xi, Amurka da Sin sun yi kyakkyawar mu’amala a fannonin kasuwanci da tattalin arziki da sauransu. Yana gamsuwa da nasarorin da Sin ta samu, kuma bangaren Amurka yana son kara yin hadin gwiwa da bangaren Sin don kara inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Kazalika, Donald Trump ya ce yana dora muhimmanci matuka kan damuwar da bangaren Sin ke da shi kan batun Taiwan, kuma yana fatan kara tuntuba da bangaren Sin, don tabbatar da ganin an ci gaba da raya kyakkyawar huldar bangarorin biyu cikin kwanciyar hankali a cikin wa’adinsa. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link