Gobarar Singa: Ba za mu yarda da bayanan ƙarya ba — Gwamnatin Kano
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Kano ta gargaɗi ’yan kasuwar da gobara ta ƙone wa dukiya a Kasuwar Singa, da su guji yin ƙarya wajen cike bayanan neman tallafi daga gwamnati.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Farouk Ibrahim ne, ya yi wannan gargaɗi bayan jagorantar wani kwamiti zuwa wajen da gobarar ta lalata don tantance irin asarar da aka yi.
Yayin da yake magana da ’yan jarida bayan kai ziyarar, ya ce kwamiti ya je wajen ne domin ganin irin asarar da aka yi.
“Babban dalilin ziyartar wajen guda biyu ne. Na farko, domin bai wa membobin kwamitin damar yin bincike da ganin yadda kayayyaki suka ƙone,” in ji shi.
Ya bayyana asarar da aka yi a kasuwar a matsayin abu mafi girma kuma ya tausaya wa waɗanda abin ya shafa.
“Za ku iya ganin girman yadda abubuwa suka lalace. Baya ga asarar rayuka, irin wannan shi ne mafi munin abin da mutum zai iya fuskanta.
“Muna addu’a Allah ya bai wa ’yan kasuwar da abin ya shafa ƙarfin jure wannan asara. Babu wanda zai iya maye gurbin abin da ya rasa gaba ɗaya, amma za mu yi ƙoƙari wajen bayar da tallafi,” in ji shi.
Ya ce kwamiti ya isar da saƙo game da bayyana bayanan gaskiya game da rabon tallafin, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da yaƙi da cin hanci da rashawa.
“Wannan kwamiti ya ƙunshi mutane masu ƙima a idon jama’a. Ba za mu yi rashin gaskiya ba a aikin da aka ba mu,” in ji shi.
Ya gargaɗi ’yan kasuwa da kada su bayar da bayanan ƙarya domin samun tallafi.
“Mun isar da saƙo ga ’yan kasuwa musamman waɗanda abin ya shafa cewa ba za mu yarda da rashin gaskiya ba. Ba za mu bari wani abu ya hana amfani da kuɗaɗen da aka bayar don tallafa wa jama’a ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa duk wanda aka kama yana ƙoƙarin yi wa tsarin zagon kasa zai fuskanci hukunci.
“Kamar yadda wakilin EFCC ya faɗa, mafi ƙarancin hukuncin da mutum zai fuskanta shi ne rasa tallafin da zai samu. Mafi tsanani kuma shi ne a ɗaure shi. Wannan shi ne muhimmancin aikin da muke yi,” in ji shi.
“Bai dace wani a cikin kwamiti ya bar mutane su ci gaba da rayuwa cikin wahala ba. Idan ba za mu iya taimaka wa masu buƙata ba, ba za mu azabtar da su ba,” in ji shi.
Sakataren, ya kuma roƙi ’yan Najeriya su taimaka wa waɗanda abin ya shafa, inda ya ce asarar ta zarce adadin kuɗaɗen da aka tara musu.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta bayar da Naira biliyan biyar, yayin da Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, ta bayar da gudunmawar Naira biliyan uku, sai kuma wasu ɗaiɗaikun mutane da suka bayar da nasu tallafin.
“Yawan abin da aka yi asara ya wuce tunanin mutane. Bincike ya nuna cewa asarar da aka yi ta haura Naira biliyan 20. Muna roƙon ’yan Najeriya da su taimaka wa ’yan kasuwar nan,” in ji shi.
Ya tabbatar wa masu bayar da tallafi cewa Gwamnatin Kano, ta buɗe asusu na musamman don karɓar duk wani tallafi tare da alƙawarin yin komai cikin gaskiya.
“Muna tabbatar wa al’ummar Kano da Najeriya cewa duk abin da aka bayar zai isa ga ’yan kasuwar da abin ya shafa. Za mu bayar da cikakken bayani kan duk kuɗaɗen da aka karɓa da yadda aka raba su,” in ji shi.
Gobarar ta ƙone shaguna da kayayyakin biliyoyin Naira, lamarin da ya sanya ’yan kasuwa dama cikin tsaka mai wuya tare da neman tallafi daga jama’a.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link