Ban ɓata zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff
[ad_1]
Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya taɓa zargin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ƙirƙiro Boko Haram.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sanata Sheriff ya bayyana labarin a matsayin ƙarya mara tushe.
Ya ce bai taɓa yin wata hira ko yi wa wani bayani da ya shafi Shettima game da kafa Boko Haram ba.
“Wannan labari ƙarya ne gaba ɗaya, kuma an shirya shi ne domin rikita jama’a da kawo rabuwar kai,” in ji sanarwar.
Sheriff, wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya ce waɗanda suka yaɗa wannan labari suna ƙoƙarin rage ƙimarsa da kuma ɓata gudunmawar da yake bayarwa wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai a Jihar Borno da Najeriya baki ɗaya.
Ya ce ya umarci lauyoyinsa su gano waɗanda suka yaɗa labarin tare da ɗaukar matakin shari’a a kansu.
“Idan ba a gaggauta goge wannan labari daga kafafen da suka yaɗa shi ba, zan ɗauki matakin shari’a,” in ji Sheriff.
Sanata Sheriff, ya roƙi ’yan Najeriya da kafafen watsa labarai da su yi watsi da labarin, tare da bin gaskiya da adalci wajen yaɗa bayanansu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link