An kashe malamin da ya yi hasashen Daular Isra’ila za ta rushe nan da 2027 — Sheikh Yelwa

[ad_1]



Fitaccen Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Farfesa Mansur Isa Yelwa, ya ce an kashe malamin da ya yi hasashen cewa Daular Isra’ila za ta rushe nan da shekarar 2027.

Farfesa Yelwa ya ce tun a shekarar 1998 ce a wata hira da da kafar Al Jazeera ta yi da malamin mai suna Sheikh Ahmad Yasin, ya yi hasashen cewa Daular Isra’ila za ta rushe zuwa 2027, bayan nazari kan tarihin daulolin Banu Isra’ila

A cewar Sheikh Yelwa, binciken ya nuna cewa a tarihin Banu Isra’ila, galibi daulolinsu kan ɗauki kusan shekaru 40 kafin su rushe, sannan a sake kafa wata.

Malamin ya ƙara da cewa, kimanin shekaru biyar bayan wannan hasashe ne aka kashe Sheikh Ahmad Yasin, yana mai cewa kisan na iya kasancewa yana da alaƙa da irin wannan ra’ayi da ya bayyana.

Yelwa ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ya ce ya gudanar da bincike mai zurfi kan tarihin daular Isra’ila.

Malamin ya bayyana haka ne yayin da kafar Al Jazeera ta yi wata hira da shi, inda ya ce ya yi bincike mai zurfi a kan yadda daular Isra’ila take kasancewa tsawon shekaru, inda ya ce su Banu isra’ila galibi shekara 40 suke yi daularsu ta rushe, sai dai su sake kafa wata.

Yelwa ya ƙara da cewa, tun bayan fitar wannan rahoto ne shekara biyar baya aka kashe malamin, wanda kisan malamin ba ya rasa nasaba da wannan hasashen nasa.

Yelwa ya bayyana haka cikin wani faifan bidiyo na karatunsa da ke yawo a kafafen sada zumunta na intanet.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *