Xi Jinping Ya Amsa Wasikar Tsoffin Sojojin Zimbabwe
[ad_1]
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar tsoffin sojojin gwagwarmayar ‘yantar da kasar Zimbabwe. Cikin sakon da ya mayar a Larabar nan ga tsofaffin sojojin, shugaba Xi ya ce, “Kun bar gidajenku kun shiga cikin babban aikin ‘yantar da al’umma a lokacin da kuke matasa, inda kuka kulla dangantaka mai zurfi da Sin ta hanyar gwagwarmaya iri guda, kuma har yanzu kuna mayar da hankali kan abota tsakanin Sin da Zimbabwe, da kuma tsakanin Sin da nahiyar Afirka, hakan yana motsa rai na, ya kuma burge ni sosai”.
Xi ya jaddada cewa, shekarar nan ta 2026 ita ce ta cika shekaru 70 da kaddamar da dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da Afirka, kuma ita ce “Shekarar musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka”. Cikin shekarun 70 da suka gabata, Sin ta kasance abokiyar gwagwarmaya, kuma abokiyar hadin gwiwa mai nagarta a aikin ‘yantar da al’umma, da farfado da ci gaban Afirka, tare da abokai na nahiyar Afirka dake mutunta juna, da tallafa wa juna, da hadin gwiwa don magance wahalhalu, da tinkarar kalubaloli tare don zamanantar da al’ummunsu tare.
Shugaba Xi ya kara da cewa bangaren Sin yana son yin hadin gwiwa da bangaren Afirka, don ci gaba da bunkasa abotar gargajiya, da kafa kyakkyawar makomar al’ummun bangarorin biyu mafi haske tare. Sin na fatan Zimbabwe za ta karfafa gwiwar karin matasan Afirka, wajen shiga aikin habaka abota tsakanin Sin da Zimbabwe, da kuma tsakanin Sin da Afirka.
Bayan kafuwar jamhuriyyar jama’ar Sin, Sin ta kasance mai goyon baya ga yakin da Afirka ke yi da mulkin mallaka da kuma ‘yantar da al’umma. A kwanan nan ne tsoffin sojojin gwagwarmayar ‘yantar da Zimbabwe, sun rubutowa shugaba Xi Jinping wata wasika, suna godiya sosai ga goyon baya mai kima na kasar Sin ga aikin ‘yantar da al’ummar Zimbabwe, suna kuma yabawa manyan nasarorin da al’ummar Sin ta samu a sabon zamani, tare da nuni cewa za su himmatu wajen ci gaba da zurfafa abota tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link