Ko Kin San… Hanyoyin Kula Da Lafiya Da Safe?
[ad_1]
Farawa da addu’ar tashi daga barci.
Domin hakan yana sa kwakwalwa ta fara aiki cikin nutsuwa. Sannan yana rage damuwa tun da safe.
Shan ruwan dumi, domin yana motsa hanji, da tsarkake jiki daga guba. Yana hana bushewar baki da fata.
Wanke fuska da baki da farko da Brush da makilin mai fluoride. Goge harshe domin kawar da wari. Hakan na rage taruwar kwayoyin cuta.
Ko da ba za ka ci abinci a lokacin ba, wanke baki da safe dole ne. Ka motsa jiki na minti 3 zuwa 10. Ka mike ko dan yawo, domin yana farfado da jini. sannan yana rage ciwon baya da kasala.
Cin abinci marar nauyi, kamar: Ayaba, Tuffa, yagot, ko kankana.
Irin wannan abinci yana motsa kwakwalwa da ciki. Tsaftace jiki ta hanyar wanka, domin yana tayar da kuzari, kuma yana hana wari da taruwar gumi bayan bacci.
Shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantajewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu iyayen ba sa iya koya wa yaransu mata aikace-aikacen gida kamar su; Shara, wanke-wanke, wankin ‘toilet’, wankin kayan sakawa kanana, gyaran ‘Kitchen’, girki, da dai sauransu. Har sai idan auransu ya gabato sannan a lokacin za a fara kokarin koya musu.
Wannan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Ko me za a ce game da hakan?, Ko akwai wasu matsaloli da za ta iya fuskanta a gidan aure game da hakan, musamman yadda aka koya mata a kuracen lokaci?, wadanne hanyoyi ya kamata iyaye su bi wajen koyawa yaransu mata yadda za su iya aikace-aikacen gida ba tare da sun sha wahala ba?”.
Ga dai bayannan nasu kamar haka;
Kula da fata (skin care)
Yin amfani da moisturizer. Yin shiga wadda ta dace idan za ka fita rana. Wannan yana hana tsufa da kuma kara lafiyar fata.
Tsara ayyukan rana. Yana rage cunkoson ayyuka, ka guji wayar hannu nan da nan bayan tashi daga bacci, hakan yana rage damuwa.
Sannan yana ba kwakwalwa damar samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Fesa turare da bude tagogi, yana shigar da iska mai kyau, yana taimakawa wajen magance ciwon kai da kasala.
Me Ya Kamata Ka Gujewa Da Safe?
Cin/shan kayan zaki, shaye-shayen lemon dake da zaki, rashin wanke baki.
[ad_2]
Source link