Ganduje ya dawo Najeriya yayin da ake dakon sauya sheƙar Gwamna Abba zuwa APC

[ad_1]



Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo Najeriya bayan shafe makonni yana hutu a Birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Hadiminsa, Malam Muhammad Garba, ya sanya wa hannu.

A cewar sanarwar, Ganduje ya isa Filin Jirgin Saman Murtala Muhammed da ke Jihar Legas a ranar Asabar da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, a jirgin Emirates Airline.

Ana sa ran zai wuce Abuja kai-tsaye domin tattauna wasu tsare-tsare game da APC a Kano.

Bayan dawowarsa, Ganduje zai fara gudanar da taruka da shugabannin jam’iyyar da sauran manyan masu ruwa da tsaki.

Taron zai mayar da hankali ne kan sabbin sauye-sauyen siyasa a Jihar Kano.

Garba, ya ce abubuwan da za a tattauna a taruka za su mayar da hankali kan halin da siyasar jihar ke ciki tare da ƙarfafa haɗin kai a Jam’iyyar APC, musamman a Kano.

Ya ƙara da cewa hakan ya nuna ƙudurin Ganduje na ci gaba da tattaunawa da haɗin gwiwa a jam’iyyar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Ganduje zai halarci shirin fara rajistar mambobin APC ta intanet a faɗin ƙasa, wanda aka ƙaddamar a lokacin da yake Shugaban Jam’iyyar na ƙasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa tsohon gwamnan na nan daram wajen ƙarfafa tsarin jam’iyyar da bunƙasa dimokuraɗiyya a APC.

Dawowarsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *