An Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama, An Tarwatsa Sansanoninsu A Dajin Kogi — ‘Yansanda
[ad_1]
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kogi ta ce ta yi nasarar dakile munanan hare-haren ‘yan bindiga, ta katse hanyoyin ta’addancinta, sannan ta wargaza sansaninsu bayan fatattakarsu a wani hare-haren hadin gwiwa na rundunar ‘yansanda da sojoji a jihar.
‘Yansandan sun ce, rundunar ‘yansandan Nijeriya ta samu goyon baya ne daga rundunar sojin saman Nijeriya.
- Tarihi Ba Zai Manta Yadda Amurka Ke Zubar Da Jini Da Murƙushe Haƙƙin Ƙasashen Latin Amurka Ba
- An Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama, An Tarwatsa Sansanoninsu A Dajin Kogi — ‘Yansanda
Jihar Kogi, musamman ma yankunan dake yammacinta sun fuskanci hare-hare masu tsanani daga ‘yan bindiga, wadanda ake zargin an koro su ne daga jihohin makwabta, wadanda ke da iyaka da jihar.
An sace mutane da dama, ana zargin an biya miliyoyin kudin fansa domin kuɓutar da ‘yan uwa yayin da wasu kuma da dama sun mutu a hannun ‘yan bindiga a jihar.
Sai dai, gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Usman Ododo, ya ci gaba da nanata kudirinsa na yaki da rashin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yin sulhu da wani ɗan ta’adda ba.
A sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kogi, CSP William Ovye Aya, ya fitar a ranar Lahadi a Lokoja, ya ce, ci gaba da kai hare-haren kan ‘yan bindiga a jihar da rundunar hadin gwiwa ta ‘yansanda da sojoji ke kai wa ya haifar da sakamako mai kyau.
[ad_2]
Source link