Mutum 12 sun nutse bayan sake kifewar jirgin ruwa a Sakkwato
[ad_1]
An sake samun damuwar kifewar jirgin ruwa a Ƙaramar hukumar Shagari inda jirgin ruwa ya nutse da mutane 12 a Ƙaramar hukumar ta Jihar Sakkwato wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu namiji da mace sauran 10 suka samu raununka.
Hatsarin ya faru ne da daren ranar Alhamis a gulbin Shagari inda mutane suka shiga cikin damuwa da kaɗuwa kan jirgin daya nutse da mutane da babur guda biyu da sauran kayan amfani, a wata ɗaya jirgi uku ya nutse a ruwa a Sakkwato.
Nasir Umar wanda lamarin ya faru gaban idonsa ya ce, “jirgin ya nutse da mutane 12 da ya ɗauko daga garin Jaranja zuwa Ruggar Buda a mazaɓar Lambara, kan hanyar ne ya kife a daren Alhamis aka fitar inda mutum biyar sun samu rauni.
“Mutanen gari da suka kawo ɗauki ne suka taimaka kuma su ne suka ci gaba da aikin harranar Jumu’a, an yi nasarar fitar da mutum shida, biyar a raye ɗaya ya mutu, mace guda ta bata ba a ganta ba.
“Kan zurfin ruwan har yanzu ba a samu ceto mace daya da ta rage a ruwan ba, ana dai sa ran ba ta da rayuwa a yanzu,” a cewarsa.
Ya yi tir da halin da gwamnati ta nuna kan lamarin in da har aka ciro mutanen ba wani wakilin gwamnati da ke wurin, mutane ne suke taimakon junansu a gaban Sarkin Ruwa.
Kabir Lumu ya nuna kifewar jirgi da ake samu a kwanan nan sakaci ne na gwamnati domin ta ƙi samar da hanyoyin mota a wuraren da ruwa suka mamaye kuma sun ƙi samar da tsari mai kyau a harkar sufurin jiragen, sun ƙyale talakawa suna kowa tasa ta fishshe shi, matuƙar Gwamnatin Sakkwato ba ta dawo cikin hayyacinta ba kan wannan matsalar za a ci gaba da rasa mutane a jirgin ruwa.
A lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin mai bai wa gwamnan Sakkwato shawara kan Hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha, Aminu Liman Bodinga ya ce sun tura jami’ansu inda lamarin ya faru don ba da taimakon da ake buƙata.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link